Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha shida

Shin rukiyya na fitar da Aljanu ya halatta?
TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, mutum ne ya mutu ya bar matarsa da ciki, bayan watanni sai ta haihu. sai wasu ke cewa dan bai zo da rai ba, wasu kuma suka ce ya yi kuka, shin wannan dan yana da gado?
Daga Isah Ibrahim Jahun
SHAIKH ZAKZAKY: Tun da ana rigima ne a kan ya yi kuka ko bai yi ba, to sai a koma Ga hanyar da za a iya tantancewa. Domin in ya tabbata ya zo da rai ne yake da gado. In kuwa ya riga ya mutu a ciki kafin ya fito, to ba ya da gado. Saboda haka sai a koma hanyar da za a iya tantancewa, wannene ba wannene ba. In ya tabbata ya mutu a ciki, to shi kenan ba shi da gado din kenan. In kuwa ya tabbata ya fito da rai, amma ya rasu, to za a raba gado da shi. (Tantancewa, shi ne) idan akwai shaidu da suka shaida sun ji kukan, adilai, za a iya yarda da shaidarsu. In ba shaida, kamar misali, ita kadai da ta haihu, ba kowa kusa da ita, sai ta raya cewa ya yi kuka, sai aka sa shakku, to shi kenan sai a rantsar da ita. Wato ko shaidu ko rantsuwa.
TAMBAYA: Mutum ne ya dade yana rashin lafiya har ta kai sai dai a kwantar a tayar na tsawon shekaru. Wani lokacin ya yi sallah ko azumi, wani lokacin kuma ba ya yin su, har Allah ya karbi ransa, to yaya hukuncin wannan azumin da sallar a wajen magadansa?
Daga Isah Ibrahim Jahun
SHAIKH ZAKZAKY: Azumin da sallar, in dai ciwon ba yana raba shi da hankalinsa bane, to zai zama ya hau kansa ya yi. Sai dai lokacin sallar da ya zo tsananin rashin lafiyar ya kai ma ba shi cikin hankalinsa, ita ce kawai ta fadi. Saboda haka sai su tantance salloli da azumummukan da suka hau kansa bai yi ba, in ya rasu sai su biya masa. Wanda kuma ya hau kansa wajibi ya yi, shi ne babban dansa na fari. Dansa na fari shi ne ya hau kan sa wujuban. Ba lalai ya yi mubashar, da kansa ba, yana iya daukar dawainiyar wani ya yi masa, kamar ya biya wani lada ya yi masa. A takaice dai wannan ya hau kan magajinsa, shi ne babban dansa namiji. Ya yi da kansa ko kuma ya biya lada a yi.
TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, mene ne hukuncin aiki a bankin da ake mu'amalar ruwa da kuma kotun da ba a yin shari'ar Musulunci?
Daga Ya'u Saidu Jahun Jigawa.
SHAIKH ZAKZAKY: Mun sha amsa irin wadannan tambayoyin. Don haka sai ka duba amsar da aka bayar a baya.
TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, mutum ne ya je bakunta sai janaba ta kama shi kuma ba zai iya wanka ba ko don sanyi ko kuma saboda ba mai iya dafa masa ruwa kuma ba zai iya tambaya ba, amma zai iya yin alwala, to yaya zai yi?
Daga Kabir M. Nasir Samaru Zariya
SHAIKH ZAKZAKY: Alwala ba ta tsaya wa a matsAyin wanka. Saboda haka idan wanka ya hau kan mutum, zai iya yin alwala don ya halatta masa cin abinci da shan ruwa, amma ba ya tsayawa a matsAyin wanka. Saboda haka in zai yi salla dole sai ya yi taimama domin bukatar salla. Na'am akwai alwala, amma don halasta ci da barci, wanda suke makaruhi ne ga mai janaba ya yi har sai ya yi wanka. Amma in salla ta kama shi, kamar yayin da ya ambata, wanda yake akwai tsananin wahala ya yi da ruwan sanyi, kuma ba zai yiwu ya yi ba sai ya sami ruwa mai dumi. In lokacin salla ya yi, to taimama zai yi. Alwala bai tsaya wa a matsayin wanka, amma ana iya alwala da nufin halatta cin abinci ko shan ruwa ko barci, wadanda suke makaruhi ne ga mai janaba. Kuma in salla ta kama a daidai wannan hali, to dole sai ya yi taimama.
TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, ina hukuncin matar da mijinta ya neme ta, amma ta ce sai ta yaye danta?
Daga Aminu Ahmadu T/Wada Makarfi
SHAIKH ZKZAKY: Abin da za mu ce shi ne ba ta samu ta yi haka nan ba. Mace ba ta samu ta hana wa mijinta kanta ba a yayin da ya bida. Hujjar cewa tana raino ba hujja bace, tunda ba a ce in ana raino namiji ba ya kusantarta ba. Allahumma sai dai idan tana son ta ja hankalinsa da su yi yarjejeniya don gudun samun gwarne. To sai su san dibarar da za su yi wajen hana daukar ciki, in ba su bukata. Amma wannan dole ya zama ba ita ta shardanta masa ba, shi da ita ne suka yarda a kan haka nan. Ko da kaurace wa saduwa ko da yin saduwar da zai hana daukar ciki, kamar dibarar amfani da kwaroron roba, ko azalu, ko wani abu mai kama da haka. Amma dole wannan ya zama sun yarda a tsakaninsu. Ta kowane hali dai ba ta samu ta hana kanta da wannan hujja ba.
TAMBAYA: Ina hukuncin matar da ta tambayi mijinta za ta unguwa ya hana, amma iyayensa suka ce ta tafi?
Daga Aminu Ahmadu T/Wada Makarfi
SHAIKH ZAKZAKY: Hakkinsa ne dai shi miji ya ba matarsa damar fita ko ya hana ta. Amma wala'alla sai dai a je a babin maslaha, kasancewa in shi yana da uba, shi kuma ubansa yana da girma gare shi. Saboda haka yana iya saurara masa. A babin maslaha, ba babin hakki ba. Idan ubansa ne ya ce ta tafi kawai, ka ga sai ya yi shiru don girmama mahaifinsa. Amma ba wai a shari'a ta ce shi uban yana da hakkin ya yi haka nan ba.
TAMBIHI: In mutum ya ce ina hukuncin kaza sai ka rasa yadda za ka amsa masa. Hukunce-hukuncen shari'a guda shida ne ko mu ce biyar. Wajibi, haramun, makaruhi, mustahabbi, halas. Wadannan sune hukunce-hukunce. Saboda haka in ka ce ina hukuncin kaza zan dauka hukunce-hukuncen kake nufi, in ce maka kaza.
TAMBAYA: Mene ne hukuncin mutumin da aka sami Alkur'ani a takalmansa bai sani ba?
Daga Aminu Ahmadu T/Wada Makarfi
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai in dai ana nufin ya taka Alkur'ani ba da sani bane, tunda da rashin sani ne, ba komai. Sai dai in an gano, shi kenan sai a cire Alkur'anin daga cikin takalma din. Allah ya kiyaye.
TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, ina neman bayani ne game da azumin watan Rajab da Sha'aban?
Daga Abdulkadir S. T/Mafara Zamfara
SHAIKH ZAKZAKY: Eh haka ne, a cikin babin falaloli. Ya zo cewa akwai falaloli masu yawan gaske ga azumin wadannan watanni biyu. Mutum yana iya yin iya wanda yake iyawa, iya kokarin duk da ya yi, yana samun lada. Ya zo a hadisi ewa Manzon Allah yana yawaita azumi a watan Sha'aban, har ma an ce yakan azumce shi ne ma duka. Kuma akwai ruwayoyi da suka nuna falalar azumin Rajab tun daga daya har talatin ga wata. Alal misali in ya duba Ikbal, zai ga falalar azumin kowace rana, tun daga daya har talatin, kowanne ga falalarsa. Saboda haka idan mutum ya yi azumin yana da lada. Muna iya cewa Mustahabbi ne.
Sai dai an so kada mutum ya fara yin azumi gab da Ramadana, in da can ma ba yana yi bane. Amma in da can yana azuminsa har Ramadan ya zo yana yi, duk ba laifi. Amma gab da Ramadana, in ba yana yi bane ba a son ya yi, sai ya jira sai Ramadana ya zo.
TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, ina son a yi mani bayani game da halasci ko haramcin yin rukiyya na fitar da aljannu.
Daga Alhaji Shehu Usman Mairuwa Funtuwa
SHAIKH ZAKZAKY: Addu'a kenan ni na fahimta, shi kuma addu'a wani sanannen abu ne. (In dai addu'a kenan), sai mu ce halas ne. Ana addu'a domin korar aljannu. Kuma akwai Ma'asurat ma har da wanda aka ruwaito daga wajen Annabi. Alal misali akwai wanda ya je wajen Annabi yana cewa Aljanu sun dame shi a gidansa, Manzon Allah ya rubuta masa wata wasika ya zuwa gare su, ya ce ya sa a gidan. To sai ya zo yana ba Mazon Allah labarin suna ta kururuwa, suna cewa a cire masu wannan don Allah. Sai ya ce ba ni cire maku sai na je wajen Manzon Allah ya umurce ni da haka nan. Sai ya ce, ai da ka cire masu saboda tsananin da suke samu. Wanda ya nuna kenan wato tun da har ma an ruwaito irin wannan wurin Annabi, akwai wani abu mai kama da haka nan kenan. Sai dai ba ina cewa duk abin da wadansu ke yi da cewa suna cire Aljanu, shi ne wannan ba. Tun da wasunsu suns riyawar suna cire Aljannu, mutum yana fama da zazzbin Maleria su zo su yi ta karance-karance, su ce wai suna cire masa aljannu ne, alhali Maleria ce kawai, da ma an yi allurar 'chloroquine' ne da ya warke. Galiba wadanda suke yi din ba su da tabbacin cewa ko aljannun ne ma.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved